Ko Wane Ne Kwamishina Wakili? Daga Abokin Karatun CP Wakili Kwamishinan 'Yansanda Yaya Yelwa Wakili zai yi murabus daga aiki bisa shekarunsa da kuma karewar wa'adin shekarun aikinsa a 'yan makonni masu zuwa. Wannan jami'in ya dade yana aiki a karkashin yaransa; wato wadanda ya girme su a aiki wadanda suke ba sa iya gyara wasu kura-kuren 'yan siyasa sukan makance don kwadati wanda shi kuma ba shi yake bukata ba aikinsa kawai ya sani.
Wasu ya riga su soma aikin 'yansanda an ba su mukamin DIG har sun yi murabus, a yayin da sa'o'insa a aiki tuni suka zama IGP. A halin da ake ciki ma wasunsu sun tara magudan kudade a asusun ajiyarsu na banki sun mallaki kaddarori marasa adadi. Za a iya cewa hukuncin ubangiji ne kawai ta sanya ya zama kwshina a jihar Katsina wanda a yanzu yake Kano, wanda a yanzu tauraronsa take haskawa a idon duniya, kai za a iya cewa shi ne dansada daya tilo da ake alfahari da shi a Najeriya. A bisa al'ada 'yansanda ire-irensu akan ajiye su ko ta kwana a turasu inda lamura suka baci, da zarar sun gyara lamuran sai a sauya su a kawo wadanda ake bukata.
Sun tura sa Kano ne don su ga gazawarsa, da yake Allah ba azzalumin kowa ba ne! sai Allah ya nuna ba karshensa kenan ba. Yaya Yelwa zai yi murabus ya koma Gombe wajen mutanesa su rika zundensa suna cewa ina gaskiyar ta shi da zai kawo masu, za su tuna mashi da cewa mahaifinsa Atiku da ya yi aiki da hukumar Customs har ya yi murabus ya kuma mutu bai tara komai ba duk da damarmakin da ya samu ya ki amfani da su. Lallai za su tabbatar masa da cewa talauci a jininsu yake. Na sansshi sani na hakika domin mun shafe shekaru 4 da rabi da shi a jami'ar Maiduguri. Yaya Yelwa yakan rarrabawa mutane kudin tallafin karatunsa(schol arship) ga masu bukata kai har yakan rasa kudin da zai ci abinci da shi. Mashin dinsa har ana ma shi lakadi da (People’s Honda) wato na kowa. Ba shi da kow illa matarsa da yaransa domin su kadai ne kawai suke iya hakuri da shi. Zai bar aiki da fansho wanda ba zai iya biyan kudin katin wayarsa ba, da sanya mai a motarsa da ciyar da iyalansa ba a watan. Aikin da ya yi ya sadaukar da rayuwarsa ne kawai wajen tsare gaskiya da kare mutuncin wasu da kuma daga darajar aikin 'yansanda wadanda wasunsu suke ce masa to sai ka je ka ci gaskiyarka idan ka gama aiki. Hakan ta faru da shi a lokacin da yake aiki da EFCC inda aka tura shi aiki a karkashin wadanda ya fi su mukami har su biyu. Wannan Najeriya kenan. Akwai dubannin irin su Muhammad Alkali da aka yi asararsu wadanda ba a ko damuwa da su ko da da rana daya. Abun haushi Wakili ba zai yi murabus a matsayin AIG ba. Amma Allah ya san hikima da dalilin haka, al'ummar jihar Kano na san za yi layi tun daga Kano zuwa Gombe don girmama shi, Insha Allah! Muna alfahari da kasancewar Muhammad Wakili cikinmu 'yan shekara 1982 a jami'ar Maiduguri.