Daga kasar Nijar, wasu dalibai sun nuna murnar su ga nasarar Buhari Adamu Haruna Ahmad ya bayyana mana cewa daliban sun shirya taron ne domin taya shugaba Muhammdu Buhari murna.
Wasu Daga cikin Daliban Najeriya da suke karatu a jami’ar Maryam Abacha dake garin Maradi a chan kasar Nijar, suma sun bayyana farincikinsu bisa lashe zaben shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu.
An cigaba da nuna farinciki ga samun nasarar shugaban Muhammadu Buhari da ake tayi a cikin kasa Najeriya dama sauran sassan duniya inda ‘yan Najeriya suke zaune a wadancen kasashe, ko dai domin karatu, kasuwanci ko wani nauyin al’amari na rayuwar yau da kullin. div class="separator" style="clear: both; text-align: center;">